Muna zaune ne a cikin ɗaya daga matsattsun gidajen da ke rukunin gidaje mai hawan bene da yawa wanda ke matsayin wurin zama ga iyalai masu matsakaicin samu da dama. Sai dai kuma, iyalin Kyanwar Gida da suka tare a rukunin gidajen yawansu zai iya ninka na mutanen da ke rayuwa a ciki. Saboda waɗannan dabbobi masu lanƙwasassun farata, waɗanda za su iya kama da iyalan dabbobi irin su – Zakuna, da dangogin Damisa daban-daban ba sa tsoron kowa a farfajiyarmu. Ƙaruwar yawan kyanwoyi masu farata tara a yatsunsu abu ne da ya dami kowane mutum inda kuma ya kasance abin raha da mutane masu yawa. Waɗannan kyanwoyi da ke layinmu suna da wani tsari na yankin mallaka in da babu wanda ke shiga na wani. Gidan ƙasa, hawa na farko da na biyu na masu farautar beraye ne kuma ba sa barin yankunansu sai dai na ‘yan lokutan da sukan ƙetare iyaka su shiga ɗakunan girki. Baranda kuwa musamman ta ƙanana ce inda kuma lokaci zuwa lokaci manya daga dangin kyanwoyi na Siam suke amfani da shi don lasar jiki da shan hantsi. Wasu daga cikin mazajen kan sami lafiyayyun lungunan su yi ta sharar barci a wuraren da babu sararin jawo kyanwa ciki, kamar ɗakin maigadi, inda za su iya tarar da bawan Allan yana jan minshari. Allah ya yi wa waɗannan kyanwoyi da salon murya iri biyu ɗaya don yi gurnani ɗayan kuma don yin kuka da shi saboda haka wasu ‘yan tsiraru daga mawaƙan kyanwoyin da ke yankinmu su ke hana gabaɗayan mazauna wurin barci da tarukansu na dare a wasu lokuta na musamman. Wasu daga mazauna rukunin gidajen waɗanda ke son zama fes fes a siga kamar kyanwa su kan ji haushi yayin da waɗannan toka-tokar kyanwoyi suka yamutsa musu kaya. Masu zafin rai cikin mazauna wurin suna ganin ba makawa sai an yi waje da waɗannan kyanwoyi da bulala mai baki tara. Amma ‘yan a-zauna-lafiya ba su yanke hukunci ba tukuna suna jiran su ga ta inda kyanwa za ta ɓullo. To, sai dai ba mu sani ba ko waye zai tari aradu da ka! | Entry #32732 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
11 | 2 x4 | 1 x2 | 1 x1 |
|
Muna zaune ne a cikin irin 'yan kananan gidajen dogayen bene wanda yawancin mutane tsaka-tsaki ke zama. Amma, magunan da ke son zama a wajen har sun fi mutane yawa. Saboda wadannan dabbobi masu farata, yan uwa ga namun daji irinsu Zaki, Damisa da ire-irensu ba sa jin tsoron kowa. Wadannan halittu da akewa lakabin "mage mai rai tara" suna damun kowa amma kuma su na bada wani sauki ga mutane da dama. Magunan da ke layin mu, kowacce ta san iya muhallinta. A hawa na kasa da benen farko da na biyu, magunan ba su cika fita daga inda su ke ba idan dai ba sun dan kewaya neman abinci a wasu madafu ba. A kan baranda yawanci kanana maguna ke zama idan ba tsoffin maguna da ke kwanciya suna ta lashe jiki ko shakar hantsi ba. Yawancin manyan magunan kuwa na labewa a lunguna inda ba za'a dame su ba su yi barci, wato kamar dakin maigadi inda zasu same shi yana barci. Allah ya yi wa maguna baiwa ta fitar da sauti na gurnani ko kuka, wasu daga cikin magunan a unguwarmu na hana mazauna wurin barci da kuka da guje-guje cikin dare. Wasu mazaunan wurin da ke burin zama a tsaftace kamar magunan, na jin haushi a yayin da magunan su ka yi kaca-kaca da wuri. Hakika shahuna da ke yanki zasu so a ce an kori duk magunan amma kuma tattabaru na dako su ga ina mage zata yi tsalle, To, amma ba mu san wa zai zo ya kubutar da magunan ba. | Entry #33695 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
8 | 1 x4 | 2 x2 | 0 |
|
Muna rayuwa a wani karamin daki a wani babban gida da yake kunshe da gidaje, Wanda ya me dauke da gidajen matsakaichin arziki, amma iyalan bera yafi yawan iyalan mutane.saboda wadannan dabbobi da manyan faratu wadanda da suke alfahari da yan uwansu - Zaki, Damisa basa tsoron kowa a anguwanmu, yawan mage da suke daukan rayuwa bera tara ya dami kowa amma ya kawo kwanciyan hankali ma mutane da dama. Wadannan magen a layinmu suna da iyakan da suke zuwa. Gidan farko da bene na biyu da na uku, bera na shawagi saidai don't yunwa sukan Shiga dakin dafa abinci su wuce iyaka. Wannan iyakan an ware shi domin wasan yara, saidai wani lokacin magidanta na zuwa hutawa da shan rana a wannan iyakan.wadansu daga cikin wadannan magen sukan yi bacci a yayin da babu dakin mage, kamar irin dakin mai gadi yayin da suke ganin wannan mage Mara galihu na hutawa, ubangiji ya albarkaci wadannan magen da murya biyu daya na kuka guda kuma na meon, kuma wadannan bera suna hana mutane bacci da buruntun su a wasu lokuta. Wasu mazaunan dake son tsabta, domin wadannan magen sunada kazanta yayin da suka bata abubuwa, marasa tausayi cikin mazauna suna ganin a kori magen da magani, amma masu tausayin cikinsu basuyi yanke shawara ba suna jira suga ta inda magen zasu gudu. Amma, bamusan was za'a kira ya ceci magen | Entry #33710 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
6 | 1 x4 | 0 | 2 x1 |
|
Muna zaune ne a garamin gida da ke cikin rukunen gidajen sama wanda ya samar da wajen zama (muhali) ga matsakaita iyalai ko alumma. Amma, Yan gidan nau'in magunan gida Wanda ya nuna sha'awa a kan man yan alammura na iya yin nasara a kan yan gidan nau'in magunan gida. Saboda yan hudu masu yatsu Wanda suna alfahari da Yan uwa- Zakuna, Damisa, Matsakaitan magunan da nau'in magunan America, suna tsoron yan kin mu. Qaruwa yan ahlin Feline suna samar da saugin rayuwa ga al'uma. Wayanan maguna a yanki mu suna da iya ko ki. Gidan gasa, da hawan farko da na biyu-beraya su ka ajiye wa kansu sai ma yun watan masu kutse suke cikin dakin dafuwa a kan iyaka. Wannan iyaka an ware wa matasa ne da wani lokutan manya masu fada aji a kin alumina da Wanda suka sha wahala a wajen horo. Wasu mazajen maguna suna samu lungunan jin dadi inda su ke jin dadin bacci inda babu dakin, kamar dakin Mai gida, inda za'a iya samun matalaucin mage yana bacci. Ubangiji yayi wa wayanan maguna baiwan nauin sauti guda biyu, daya muryan fada na biyu muryan sananya kadan daga nau'in Qungiyan magunan in yankin mu suna hana mutane bacci saboda hayaniya a wasu lokuta. Wasu mazauna yankin Wanda suke da tsatta sun saba idan miyayu/kazami maguna sun lalata abubuwa. Masu hangen nisa suna da ra'ayin a kori magunan da yazga. Amma, sauran mabiya har yanzu ba su yanke shawara ko ba, suna sauraron da nazarin wani hanya zaifi dacewa. Saboda haka, bamu san waye zai taimaki magen ba! | Entry #33487 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
---|
3 | 0 | 1 x2 | 1 x1 |
|